Jagora ya fara da taya su murnar fitowa, tare da jajen cigaba da tsare wasu daga cikinsu a daidai wannan lokacin. Yace: “Da ace duk gabadayanku aka sake ku da ya fi mana dadi, don haka muka tsammata”.
Yace tun farko mun tsammaci za a sake ku gabadaya ne. “Tun farko ma dai lokacin daka aka yi kiran (alkalin) ya ba da hukunci akan ‘no case submission’ da aka yi, abinda muka zata shi ne duk gabadaya za a saki mutane, don ba mu tsammanin za a iya tabbatar da laifi ko da guda daya daga cikin wadannan tuhumomin da ake yi. Ballantana ma ‘no case submission’ din ya nuna duk shaidar da (‘yan sanda) suka gabatar ba ma wanda ya yi magana dangane da tuhume-tuhumen da ake yi, wadansu abubuwa daban suke fadi. To amma sai muka sha mamaki an ce wai akwai ‘case’.
“To kuma abin mamaki kaga yace yau wasu ke da ‘case’ ba duka ba. Amma a wancan lokacin sai yace kowane ke da ‘case’ din. Tun shekara uku da suka wuce kenan. Da tun a lokcin sai a ce wadannan basu da case, amma sai aka ce duk su gabadayan mutum 63 ne ko? Duk gabadayansu suna da case.
“Har nake cewa ba yadda za a yi mai hankali ya sauwala cewa ana tuhumar an kashe mutum. Kuma shi wannan mutumin da aka kashe, an harbe shi ne da bindiga, kuma harsashi daya ya huda kansa ta keya, ya fita ta goshi, amma sai a ce ana tuhumar mutum 63 duk su suka yi kisa din. Wani mai hankali ma bai kamata ma ya saurari wannan ba".
Yace: “Cikin ‘case’ din da suke da shi, duk da an ce ba batun kisan kai gabadaya, amma an ce har da laifin yin taro babu izini.” Ya cigaba da cewa: “Shi (batun yin taro da izinin ‘yan sanda) bashi a cikin dokan kasar nan sam. Tuntuni an sha zuwa kotu, ba daya ba, ba biyu ba, da tuhumar an yi taro ba izinin dan sanda ba, a kore shi”.
Yace: “Akwai abinda suke ce ma ‘precedent’, an yi ba daya ba, ba biyu ba, sun ce wannan cewa neman izinin dan sanda din dokan ‘yan mulkin mallaka ne, kuma tun lokacin da Nijeriya ta samu ‘yanci wannan dokan ta daina aiki. Nijeriya ta yi tsarin mulki wanda ya ba da abinda ake ce ma ‘Freedom of expression’, da ‘freedom of association’. Kana iya bayyana ra’ayinka, kuma kana iya haduwa da wanda ka ga dama, wanda kuke ra’ayi daya”.
Ya kara da cewa: “Hatta ma, na taba jin wani dan sanda a nan Kaduna yana cewa, babu wata dokar da tace sai ka nemi izinin dan sanda kafin ka yi taro. Sai dai idan mutane ne a kashin kansu suke neman kariyan dan sanda, to shi ne za su je suce suna neman ‘yan sanda su zo su basu kariya, in suna ganin suna fuskantar barazana, amma basu bukatar izini”.
Jagora yace: “Son rai ne din ne ya bamu mamaki, na irin yadda aka yi wani abu a kanmu wanda ya saba ma dukkanin ka’ida, kuma abin mamaki ba wanda ya yi magana dangane da wannan in ba mu ne ba. Sai dai a ji daga bakunanmu”.
Ya kawo yadda aka kai kara akan waki’ar da aka kama wadannan mutane a cikinta, a wata kotu daban, aka nemi kotu ta sa ‘yan sanda su bayar da gawarwakin Shahidan da suka kashe suka sace jikkunansu. Yace: “Amma shi Jojin, sai ya yanke hukunci da cewa lallai wannan taron da ‘yan uwa suka yi bai saba wata doka ba, don suna da ‘yancin su yi taro su bayyana ra’ayinsu, tunda suna neman a saki Malaminsu ne. Haka ya fada a kotu wajen yanke hukuncin. Yace, saboda haka kashe su da ‘yan sanda suka yi laifi ne, kuma dole su ba da gawarwakin wadannan mutanen, kuma su biya ‘ramuwa’. Ya yanke wani kudi kan kowanne”.
Jagora yace, da ‘yan sanda suka ki bin umurnin kotun, sai aka sake kai kara wata kotun. Yace: “Wannan kotun (na biyu) ne suka rubuta takarda, suka ce, shi I.G ya fadi dalilin da ya sa ba zai tafi Kurkuku ba, saboda kin bin umurnin kotu! A lokacin da ya ga wannan ne yace a ba da gawarwakin. Amma bai yi maganar ‘ramuwa’ ba, har yanzu bai bayar ba”.
Yace: “Kun ga kotuna biyu da suka yi magana akan wannan ‘case’ din, sun tabbatar da cewa ba laifin da aka yi. Amma kuma duk da haka wannan (alkalin naku) yace wai akwai ‘case’ da za a amsa. Alhali wasu kotunan su ma High Court ne, sun ce ba a yi laifi ba. Baka da wani laifi don ka fito ka bayyana ra’ayinka”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda ‘yan sanda suka bude ma mutane wuta, suka kama su suka tsare, alhali suna tafiya ne cikin sahu a tsare. “Yau shekara shida cur ana tsare da su, tun July 2019 har izuwa yau, sai yau ne aka ce to 25 basu yi laifi ba. To tambaya, tsare sun da aka yi na tsawon wannan lokaci shi kuma yaya yake, tunda a karshe ba su yi laifi ba? Ko in aka tsare mutum bai yi laifi ba ba komai?”.
Jagora yace: “Ina tsammanin mutanen nan sun yi imani kuwa za su gamu da Allah? Yanzu mutane suna tunanin za su tsaya gaba ga Allah a gobe kiyama? Yanzu kai ka dinga sa hannu a ‘warrant’ ana tsare mutum har shekara shida, sannan kace bai yi laifi ba. Kana tsammanin duk zaman nan da ya yi ba tambayo? Sai ya tafi haka nan? Kana tsammanin a wurin Allah baka yi laifin komai ba?”.
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Da wadanda suka yi kamu, - ‘yan sanda kenan, da kotunan da suka tsare, da wadanda suka yi umurni da a yi, to duk za su amsa a gobe kiyama. Kuma za su ga sakamako tun a nan, kafin ranar lahira. Don Allah ba azzalumin kowa ba ne”.
Ya kuma ja hankalin ‘yan uwan da cewa: “Mun san cewa wannan jarabawa ce, kuma haka hanyar ta gada. An jarabta na farko, kuma mu ma mun san za a jarabta mu”.
Ya kara da cewa: “Shi laifin mai addini shi ne tsayawarsa akan tafarkin addini. Shi ne laifin da Muminan farko suka yi aka azabta su da nau’o’in azaba iri-iri. Har ma a cikin abinda aka koyar da mu, akwai cewa, mu roki Allah kada a jarabce mu da irin abinda aka hjarabci wadanda suka gabace mu, don an kallafa musu jarabawowi iri-iri”.
Yace, Allah Ta’ala yana cewa: Mutane suna tsammanin za su ce sun yi imani, sai a kyale su kawai? An jarabta wadanda suka gabata, kuma dole sai an jarabta su. (Saboda haka) Jarabawa ce, har in ba a yi jarabawar ba, to ya kamata mutum ya sa Ayar tambayar, (ya ce); anya kuwa a tafarki ake?”.
Ya kara da jan hankali a kan duk inda mutum ya tsinci kansa ya zama mai kokari wajen amfanar kansa da al’ummar da ke wajen. “Yana da kyau ya zama duk inda ka samu kanka, ka yi kokari ka amfana da wannan zaman wajen isar da sako daidai gwargwado, ta yadda za a amfana da kai, a amfani al’umma. Kuma tunda an koyo darussa, an samu fursa, kamar yadda wani lokaci nake fadi cewa Imam Kazim (AS), shi ne yace, ya gode ma Allah, don ya roke shi ya bashi da ma ya bauta masa. Kuma ya bashi wannan damar, tsare shin da aka yi, ya samu ya yi ibada”.
Yace: “Da ma akan ba mutum, wanda yakan samu ya yi abinda ba zai yiwu ya yi ba in yana waje ne. Tunda an hayyake wannan (jarabawar), muna fata Allah Ta’ala yasa marhaloli da za su zo nan gaba su ma su zama an hayyake. Don jarabawa ne, ba karewa yake ba, har yazuwa lokacin da za a kai ga muradi, wato shi ne a yi kyakkyawan cikawa. Insha Allahul Azeem”.
Shaikh Zakzaky ya yi albishir da cewa: “Nasara kam tabbas ne, alkawari ne na Allah, ko badade ko bajima za a yi nasara ne.” Yace: “shi kansa zaluncin nan alama ne na zai kawo karshe. Ba a taba zalunci ya dauwama ba, (ko a tatsuniya). Ka’ida ce zaunanna, zalunci bai taba dauwama ba. To kuma tunda zaluncin ya yi kaimi, aka ayyana wasu aka ce su wadannan su ne ake ganin cewa, in ba a kawar da su ba, za su kawo sauyi, (to zaluncin zai kawo karshe ne)”.
Yace: “Mun san cewa abinda suke yi din nan, zai haifar da sakamako, wanda kuma zai haifar da mummunan karshensu ne, kuma nasara ne ga wadanda aka jarabta. Wannan jarabawa ce, muna fatan Allah Ta’ala ya kambama lada. Mu ga ladan ma tun a nan, tukuici kafin na lahira Insha Allahul Azeem, bayan amfanan da aka yi da zama a wannan muhalli”.
A karshe, Jagora ya yi addu’ar Allah Ta’ala Ya karbi shahadar wadanda aka kashe, Ya kuma ba da lafiya ga wadanda suke da raunuka. Ya gaggauta kwato mana sauran wadanda ake tsare da su.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
16/Zulgada/1446
15/05/2025
Your Comment